Firistoci 21:7-8
7
“ ‘Ba za su auri matan da karuwanci ya ɓata su, ko waɗanda mazansu suka sake su ba, gama firistoci masu tsarki ne ga Allahnsu.
8
An ɗauke su da tsarki, domin suna miƙa abincin Allahnku. An ɗauka su masu tsarki gama Ni Ubangiji, mai tsarki ne, Ni wanda ya mai da ku masu tsarki.