Firistoci 20:10-16
10
“ ‘In mutum ya yi zina da matar wani, da matar maƙwabcinsa, dole a kashe su biyu da suka yi zinan.
11
“ ‘In mutum ya kwana da matar mahaifinsa, ya ƙasƙantar da mahaifinsa. Dole a kashe shi da macen, alhakin jininsu zai zauna a kansu.
12
“ ‘In mutum ya kwana da matar ɗansa, dole a kashe su biyun. Abin da suka yi haram ne; alhakin jininsu zai zauna a kansu.
13
“ ‘In mutum ya kwana da mutum kamar yadda ake kwana da mace, su biyun sun yi abin ƙyama. Dole a kashe su, alhakin jininsu zai zauna a kansu.
14
“ ‘In mutum ya auri ’ya da mahaifiyarta, mugun abu ne. Da shi da su, dole a ƙone su da wuta, saboda kada mugun abu yă kasance a cikinku.
15
“ ‘In mutum ya yi jima’i da dabba, dole a kashe shi, dole kuma ku kashe dabbar.
16
“ ‘In mace ta kusaci dabba don tă yi jima’i da ita, ku kashe macen da dabbar. Dole a kashe su; alhakin jininsu zai zauna a kansu.
Settings