15
“ ‘Kada ku yi rashin adalci cikin shari’a; kada ku nuna sonkai ga matalauci, ko ku goyi bayan mai arziki, amma ku shari’anta maƙwabci cikin gaskiya.
16
“ ‘Kada ku yi ta yawo kuna yaɗa ƙarya a cikin mutanenku. “ ‘Kada ku yi wani abin da zai sa ran maƙwabcinku cikin hatsari. Ni ne Ubangiji.