Skip to content
Firistoci 16:20-28

Ibilar Akuya Mai Laifi

Firistoci 16:20-28
20
“Sa’ad da Haruna ya gama yin kafara domin Wuri Mafi Tsarki, Tentin Sujada da kuma bagade, sai yă kawo akuya mai rai.
21
Haruna zai ɗibiya hannuwansa a kan akuya mai ran, yă furta a kansa dukan mugunta da tawayen Isra’ilawa, dukan zunubansu, yă kuma sa su a kan akuyan. Zai kori akuyan zuwa cikin jeji a hannun mutumin da aka ba shi aikin yin haka.
22
Akuyan zai ɗauka a kansa dukan zunubansu zuwa kaɗaitaccen wuri, a can mutumin zai sake shi a jeji.
23
“Sa’an nan Haruna zai shiga Tentin Sujada yă tuɓe rigunansa na lilin da ya sa, kafin yă shiga Wuri Mafi Tsarki, zai kuma bar su a can.
24
Zai yi wanka a tsattsarkan wuri yă sa rigunarsa na kullum. Sa’an nan zai fita yă miƙa hadaya ta ƙonawa domin kansa da hadaya ta ƙonawa domin mutane, don yă yi kafara domin kansa da kuma domin mutane.
25
Zai kuma ƙone kitsen hadaya don zunubi a kan bagade.
26
“Dole mutumin da ya saki akuya na azazel yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka; bayan haka zai iya shiga sansani.
27
Dole a ɗauki jini, fata, nama da kuma ƙashin bijimi da akuyan hadaya don zunubi, waɗanda aka kawo jininsu cikin Wuri Mafi Tsarki don kafara, a kai waje da sansani a ƙone.
28
Dole mutumin da ya ƙone su yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, bayan haka zai iya shiga sansani.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options