Mahukunta 2:6-10
6
Bayan Yoshuwa ya sallami Isra’ilawa, sai suka tafi don su mallaki ƙasar, kowa da nasa gādon.
7
Mutane suka bauta wa Ubangiji duk tsawon kwanakin Yoshuwa da na dattawan da suka rayu bayansa waɗanda suka ga manyan abubuwan da Ubangiji ya yi wa Isra’ila.
8
Yoshuwa ɗan Nun, bawan Ubangiji, ya mutu yana da shekara ɗari da goma.
9
Aka binne shi a ƙasar gādonsa, a Timnat Heres a ƙasar tudu ta Efraim, arewa da Dutsen Ga’ash.
10
Bayan tsaran nan duka suka rasu, sai wata tsara ta taso wadda ba tă san Ubangiji ko abin da ya yi wa Isra’ila ba.
Settings