Skip to content
Yoshuwa 8:33-35

Yoshuwa 8:33-35

33
Sai Isra’ilawa duka, da baƙi, da haifaffun gida, da dattawansu, da shugabanninsu, da alƙalansu, suka tsaya a gefe-gefen akwatin alkawarin Ubangiji, suna fuskantar waɗanda suke ɗauke da shi, wato, firistoci waɗanda su ne Lawiyawa. Rabin mutanen suka tsaya a gaban Dutsen Gerizim, rabinsu kuma suka tsaya a gaban Dutsen Ebal, kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya riga ya umarta, cewa su sa wa mutanen Isra’ilawa albarka.
34
Bayan haka, Yoshuwa ya karanta duk abin da yake a cikin Dokoki, albarku da la’anoni, kamar yadda suke a rubuce a cikin Littafin Dokoki.
35
Babu wata kalmar da Musa ya umarta da Yoshuwa bai karanta wa dukan taron Isra’ilawa ba, haɗe da mata, da yara, da baƙin da suke zama tare da su.

Nazarin nassin nan

Sharhi a kan nassin, ba aya ɗaya ba

Sauran wuraren da Nassi ya faɗi haka

  • Maimaitawar Shari’a 11:29

    Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku cikin ƙasar da za ku shiga ku ci gādonta, sai ku yi shelar albarkun nan a dutsen Gerizim, ku kuma yi na la’ana a dutsen Ebal.
    daga aya ta 33
  • Maimaitawar Shari’a 31:12

    Ku tattara mutane, maza, mata da kuma yara, da baƙin da suke zama a cikin garuruwanku, saboda su saurara, su kuma koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su lura, su bi dukan kalmomin wannan doka.
    daga aya ta 33
  • Maimaitawar Shari’a 27:11

    A wannan rana Musa ya umarce mutane,
    daga aya ta 33
  • Maimaitawar Shari’a 27:14

    Lawiyawa za su karanta wa dukan mutanen Isra’ila da babbar murya su ce,
    daga aya ta 33
  • Maimaitawar Shari’a 31:9

    Sai Musa ya rubuta wannan doka ya kuma ba da ita ga firistoci, ’ya’yan Lawi maza, waɗanda sukan ɗauka akwatin alkawarin Ubangiji, da kuma dukan dattawan Isra’ila.
    daga aya ta 33
  • Nehemiya 8:2

    Saboda haka a rana ta farko ga watan bakwai, Ezra firist, ya kawo Doka a gaban taro, wanda ya ƙunshi maza da mata da dukan waɗanda za su iya fahimta.
    daga aya ta 34
  • Nehemiya 8:3

    Ya karanta Dokar da ƙarfi daga safe har tsakar rana yayinda yake a kan dandali da yake fuskantar dandali a gaban Ƙofar Ruwa, gaban maza, mata da kuma sauran mutanen da za su iya fahimta. Dukan mutane kuwa suka saurara a hankali ga karatun Littafin Dokar.
    daga aya ta 34
  • Maimaitawar Shari’a 31:25

    sai ya ba wa Lawiyawa, waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji wannan umarni,
    daga aya ta 33
  • Fitowa 12:49

    Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ta shafi ɗan ƙasa da kuma baƙon da yake zama a tsakaninku.”
    daga aya ta 33
  • Yoshuwa 3:3

    ba da umarni ga mutane, suna cewa, “Lokacin da kuka ga akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku, da firistoci waɗanda su ne Lawiyawa, suna ɗauke da shi, sai ku tashi daga inda kuke, ku bi shi.
    daga aya ta 33
  • Yoshuwa 4:18

    Firistocin kuwa suka fito daga kogin ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji. Nan da nan da ƙafafunsu suka taɓa busasshiyar ƙasa, sai ruwan Urdun ya gangaro ya cika kogin kamar yadda yake a dā.
    daga aya ta 33
  • Yoshuwa 8:30

    Yoshuwa kuwa ya yi wa Ubangiji, Allah na Isra’ila bagade a Dutsen Ebal,
    daga aya ta 33
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options