- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Fifiko na Wanda Ya Zo daga Sama
Yohanna 3:31-36
Fifiko na Wanda Ya Zo daga Sama
31
“Wannan da ya zo daga sama ya fi kowa; wannan da ya zo daga ƙasa na ƙasa ne, yana kuma magana kamar wanda ya zo daga ƙasa ne. Wannan da ya zo daga sama ya fi kowa.
32
Yana ba da shaidar abin da ya gani da kuma ya ji, duk da haka ba wanda ya yarda da shaidarsa.
33
Mutumin da ya yarda da ita ya tabbatar da cewa Allah mai gaskiya ne.
34
Gama wannan da Allah ya aiko yakan faɗi kalmomin Allah ne, gama Allah yana ba da Ruhu babu iyaka.
35
Uban yana ƙaunar Ɗan ya kuma danƙa kome a hannuwansa.
36
Duk wanda ya gaskata da Ɗan yana da rai madawwami, amma duk wanda ya ƙi Ɗan ba zai sami rai ba, gama fushin Allah yana nan a bisansa.”
Nazarin nassin nan
Sharhi a kan nassin, ba aya ɗaya ba
- Su wane
- Ina
- Yaushe
- About
Sauran wuraren da Nassi ya faɗi haka
Yohanna 5:24
“Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai.daga aya ta 36Yohanna 1:12
Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ’ya’yan Allahdaga aya ta 361 Tessalonikawa 5:9
Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.daga aya ta 36Afisawa 5:6
Kada wani yă ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya.daga aya ta 36Yohanna 3:15
don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.”daga aya ta 36Yohanna 3:16
Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami.daga aya ta 36Yohanna 8:23
Amma ya ci gaba da cewa, “Ku daga ƙasa kuke; ni kuwa daga bisa ne. Ku na duniyan nan ne; ni kuwa ba na duniyan nan ba ne.daga aya ta 311 Yohanna 5:10
Duk wanda ya gaskata da Ɗan Allah, yana da shaidan nan a zuciyarsa. Duk wanda bai gaskata da Allah ba kuwa ya mai da shi maƙaryaci, domin bai gaskata shaidar da Allah ya bayar game da Ɗansa ba.daga aya ta 331 Yohanna 5:13
Ina rubuta waɗannan abubuwa gare ku, ku da kuka gaskata sunan Ɗan Allah domin ku san kuna da rai madawwami.daga aya ta 36Mattiyu 28:18
Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa.daga aya ta 31Romawa 1:17
Gama a cikin bishara an bayyana adalci daga Allah wanda yake ta wurin bangaskiya daga farko zuwa ƙarshe, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.”daga aya ta 36Romawa 1:18
Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu,daga aya ta 36



Bayanin Nazari
Settings