Irmiya 51:15-19
15
“Ya halicci ƙasa ta wurin ikonsa; ya kafa duniya ta wurin hikimarsa, ya kuma shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa.
16
Sa’ad da ya yi tsawa ruwan da suke sammai sukan yi ruri; yakan sa gizagizai su tashi daga ƙarshen duniya. Yakan tura walƙiya tare da ruwan sama yakan kuma saki iska daga cikin taskokinsa.
17
“Kowane mutum marar azanci ne kuma ba shi da sani; kowane maƙerin zinariya yakan sha kunya daga wurin gumakansa. Siffofinsa na ƙarya ne; babu numfashi a cikinsu.
18
Su marasa amfani ne, abubuwan ba’a ne kawai; sa’ad da lokacin hukuncinsu ya kai, za su hallaka.
19
Wanda yake na wajen Yaƙub ba kamar waɗannan ba ne, gama shi ne Mahalicci dukan abu, har da kabilar abin gādonsa, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.
Settings