Skip to content
Irmiya 24:8-10

Irmiya 24:8-10

8
“ ‘Amma kamar ’ya’yan ɓauren nan marasa kyau, waɗanda sun yi muni har ba a iya ci,’ in ji Ubangiji, ‘haka zan yi da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da sauran mutanen da suka tsira a Urushalima, ko suna a wannan ƙasa ko suna zama a Masar.
9
Zan mai da su abin ƙyama da masifa ga dukan mulkokin duniya, abin zargi da abin karin magana, abin ba’a da abin la’ana a duk inda zan kore su zuwa.
10
Zan aika da takobi, yunwa da annoba a kansu sai an hallaka su sarai daga ƙasar da na ba su da kuma kakanninsu.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options