Skip to content
Irmiya 23:4-8

Irmiya 23:4-8

4
Zan sa makiyaya a kansu waɗanda za su lura da su, ba za su ƙara jin tsoro ko razana ba, ba kuwa waninsu da zai ɓace,” in ji Ubangiji.

Alkawarin Reshe mai adalci

5
“Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan tā da wa Dawuda Reshen adalci, Sarki wanda zai yi mulki da hikima ya kuma yi abin da yake gaskiya da kuma daidai a ƙasar.
6
A cikin zamaninsa za a ceci Yahuda Isra’ila kuma zai zauna lafiya. Sunan da za a kira shi ke nan, Ubangiji Adalcinmu.
7
“Saboda haka fa, kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da mutanen ba za su ƙara cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fito da Isra’ila daga Masar ba,’
8
amma za su ce, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fito da zuriyar Isra’ila daga ƙasar arewa da kuma daga dukan ƙasashen da ya yashe su.’ Sa’an nan za su zauna a ƙasarsu.”

Nazarin nassin nan

Sharhi a kan nassin, ba aya ɗaya ba

Sauran wuraren da Nassi ya faɗi haka

  • Ishaya 4:2

    A wannan rana Reshen Ubangiji zai zama kyakkyawa da kuma ɗaukaka, kuma amfanin ƙasar zai zama abin fariya da ɗaukakar waɗanda suka rayu a Isra’ila.
    daga aya ta 5
  • Luka 1:32

    Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar kakansa Dawuda,
    daga aya ta 5
  • Luka 1:33

    zai yi mulkin gidan Yaƙub har abada, mulkinsa kuma ba zai taɓa ƙare ba.”
    daga aya ta 5
  • 1 Korintiyawa 1:30

    Saboda Allah ne kuke cikin Kiristi Yesu, shi wanda ya zama hikima a gare mu daga Allah. Kiristi shi ne adalcinmu, da tsarkinmu, da kuma fansarmu.
    daga aya ta 6
  • Irmiya 16:14

    “Amma fa, kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “da mutane ba za su ƙara cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fitar da Isra’ilawa daga Masar,’
    daga aya ta 7
  • Irmiya 16:15

    amma za su ce, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fitar da Isra’ilawa daga ƙasar arewa da kuma daga dukan ƙasashe da ya kora su.’ Gama zan komo da su zuwa ƙasar da na ba wa kakanninsu.
    daga aya ta 7
  • Ishaya 52:13

    Duba, bawana zai aikata abubuwa da hikima; za a tā da shi a kuma ɗaga shi da ɗaukaka ƙwarai.
    daga aya ta 5
  • Ishaya 9:7

    Game da girmar gwamnatinsa da salama babu iyaka. Zai gāji sarki Dawuda, yă yi mulki a matsayinsa, zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Maɗaukaki ne ya yi niyyar aikata wannan duka.
    daga aya ta 5
  • Irmiya 33:16

    A kwanakin nan zan ceci Yahuda Urushalima kuma za tă zauna lafiya. Sunan da za a kira ta shi ne, Ubangiji Adalcinmu.’
    daga aya ta 5
  • Irmiya 23:3

    “Ni kaina zan tattara raguwar garkena daga ƙasashen da na kore su zuwa zan kuma dawo da su ga makiyayansu, inda za su yi ta haihuwa su riɓaɓɓanya.
    daga aya ta 7
  • Filibbiyawa 3:9

    a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina wanda yake zuwa daga bin doka ba, sai dai adalcin da yake samuwa ta wurin bangaskiya a cikin Kiristi, adalcin da yake fitowa daga Allah da kuma yake zuwa ta wurin bangaskiya.
    daga aya ta 6
  • Zakariya 6:12

    Ka ce masa ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ga mutumin da sunansa ne Reshe, zai kuma ratse daga inda yake yă gina haikalin Ubangiji.
    daga aya ta 5
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options