Irmiya 23:25-32
25
“Na ji abin da annabawa suna cewa su da suke annabcin ƙarya a sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki! Na yi mafarki!’
26
Har yaushe wannan zai ci gaba a cikin zukata annabawa masu ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗun tunaninsu?
27
Suna tsammanin mafarkan da suke faɗa wa juna za su sa mutane su manta da sunana, kamar yadda kakanninsu suka manta da sunana ta wurin yin wa Ba’al sujada.
28
Bari annabin da ya yi mafarki ya faɗa mafarkinsa, amma bari wanda yake da maganata ya yi ta da aminci. Gama me ya haɗa ciyawa da alkama?” In ji Ubangiji.
29
“Maganata ba wuta ba ce,” in ji Ubangiji, “kuma kamar gudumar da kan ragargaza dutse?
30
“Saboda haka,” in ji Ubangiji, “Ina gāba da annabawan da suke satar maganganuna daga juna.
31
I,” in ji Ubangiji, “Ina gāba da annabawan da suke kaɗa harsunansu sa’an nan su ce, ‘Ubangiji ne ya furta.’
32
Tabbatacce, ina gāba da waɗannan da suke annabci mafarkan karya,” in ji Ubangiji. “Suna faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu na rashin hankali, duk da haka ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan mutane ba ko kaɗan,” in ji Ubangiji.
Settings