Irmiya 19:6-9
6
Saboda haka ku lura, kwanaki suna zuwa, in ji Ubangiji, sa’ad da mutane ba za su ƙara ce da wannan wuri Tofet ko Kwarin Ben Hinnom ba, amma za su ce da shi Kwarin Kisa.
7
“ ‘A wannan wuri zan lalace dabarun Yahuda da na Urushalima. Zan sa a kashe su da takobi a gaban abokan gābansu, a hannuwan waɗanda suke neman ransu, zan kuma ba da gawawwakinsu su zama abinci ga tsuntsayen sararin sama da kuma namun jeji.
8
Zan ragargazar da wannan birni in mai da shi abin reni, duk wanda ya wuce zai yi mamaki ya kuma yi tsaki saboda dukan masifunsa.
9
Zan sa su ci naman ’ya’yansu maza da mata, za su kuma ci naman juna a lokacin damuwar ƙawanya da abokan gāban da suke neman ransu za su yi musu.’
Settings