Ishaya 50:1-3
1
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ina takardar shaida na saki mahaifiyarka daga aure wadda na kora? Ko kuwa ga wanda mutumin da nake bin bashi ne na sayar da kai? Saboda zunubanka aka sayar da kai; saboda laifofinka ne ya sa aka kori mahaifiyarka.
2
Sa’ad da na zo, me ya sa babu kowa? Sa’ad da na yi kira, me ya sa babu wani da ya amsa? Hannuna ya kāsa ne sosai don fansarka? Na rasa ƙarfin kuɓutar da kai ne? Ta wurin tsawatawa kawai na busar da teku, na mai da koguna hamada; kifayensu duk sun ruɓe saboda rashin ruwa suka kuma mutu saboda ƙishi.
3
Na suturar da sararin sama da duhu na kuma mai da tsummoki abin rufuwarsa.”
Settings