Ishaya 39:4-8
4
Annabi ya yi tambaya ya ce, “Mene ne suka gani a fadanka?” Hezekiya ya ce, “Sun ga kome da kome a fadana. Babu abin da ban nuna musu a cikin ma’ajina ba.”
5
Sai Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji maganar Ubangiji Maɗaukaki.
6
Tabbatacce lokaci yana zuwa sa’ad da kome da yake cikin fadanka, da kuma dukan abin da kakanninka suka ajiye har yă zuwa yau, za a kwashe zuwa Babilon babu abin da za a bari, in ji Ubangiji.
7
Waɗansu cikin zuriyarka, nama da jininka waɗanda za a haifa maka, za a kwashe su a tafi, za su zama bābānni a fadan sarkin Babilon.”
8
Hezekiya ya ce, “Maganar Ubangiji da ka yi tana da kyau.” Gama ya yi tunani a ransa cewa, “Salama da kāriya za su kasance a zamanina.”
Settings