Ishaya 3:18-23
18
A wannan rana Ubangiji zai ƙwace abin da suke taƙama da shi, mundayensu, ɗankwalin kansu da abin wuyansu,
19
’yan kunnensu, kwandagansu da lulluɓinsu,
20
kitsonsu, sarƙar da suke sa wa damatsansu da ɗamararsu, kwalabai turare da layu,
21
da ƙawanen da suka sa a yatsotsinsu da hancinsu,
22
tufafi masu kyau, da manyan rigunansu, da mayafansu, da jakar kuɗinsu
23
da madubi, da kuma tufafin lilin da adikai, da gyale.
Settings