Ishaya 22:15-19
15
Ga abin da Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, ya faɗa, “Je, ka faɗa wa wannan mai hidima, Shebna, sarkin fada.
16
Mene ne kake yi a nan kuma wa ya ba ka izini ka haƙa kabari wa kanka a nan, kana fafe kabarinka a bisa kana sassaƙa wurin hutunka a dutse?
17
“Ka yi hankali, Ubangiji yana shirin ya kama ka da ƙarfi ya kuma ɗauke ka, ya kai mai ƙarfi.
18
Zai dunƙule ka kamar ƙwallo ya jefa ka a cikin ƙasa mai girma. A can za ka mutu a can kuma kekunan yaƙinka masu daraja za su kasance, abin kunya kake ga gidan maigidanka!
19
Zan tumɓuke ka daga makaminka, za a kuma kore ka daga matsayinka.
Settings