Ishaya 14:24-27
24
Ubangiji Maɗaukaki ya rantse, “Tabbatacce, kamar yadda na riga na shirya, haka zai kasance, kuma kamar yadda na nufa, haka zai zama.
25
Zan ragargazar da Assuriya a cikin ƙasata; a kan duwatsuna zan tattake shi. Za a ɗauke nauyin da ya sa wa mutanena, a kuma ɗauke nauyinsa daga kafaɗunsu.”
26
Wannan shi ne shirin da na yi domin dukan duniya; wannan shi ne hannun da aka miƙa a bisa dukan al’ummai ke nan.
27
Gama Ubangiji Maɗaukaki ya ƙudura ya yi wannan, wa kuwa zai hana shi? Ya riga ya miƙa hannunsa, wa zai komar da shi?
Settings