Haggai 2:15-19
15
“ ‘Yanzu kuwa sai ku yi la’akari da wannan daga wannan rana zuwa gaba, ku tuna yadda al’amura suke kafin a ɗora wani dutse bisa wani a haikalin Ubangiji.
16
A lokacin, idan wani ya tafi wurin tsibin da zai auna mudu ashirin, sai yă iske mudu goma kawai. Idan kuma wani ya tafi wurin matse ruwan inabi don yă ɗebo lita hamsin, sai yă tarar da lita ashirin kawai.
17
Na mai da aikin da kuka sha wahala kuka yi ya zama banza ta wurin saukar da burtuntuna, da fumfuna, da ƙanƙara, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,’ in ji Ubangiji.
18
‘Daga wannan rana zuwa gaba, wato, rana ta ashirin da huɗu ga watan tara, ku lura da ranar da aka kafa harsashin haikalin Ubangiji. Ku lura da kyau.
19
Akwai sauran irin da ya rage a rumbu? Har yanzu, kuringar inabi da itacen ɓaure, rumman da itacen zaitun ba su ba da ’ya’ya ba tukuna. “ ‘Amma daga wannan rana zuwa gaba zan sa muku albarka.’ ”
Settings