Skip to content
Farawa 9:1-7

Farawa 9:1-7

1
Sa’an nan Allah ya sa wa Nuhu da ’ya’yansa maza albarka, yana ce musu, “Ku haifi ’ya’ya, ku ƙaru, ku kuma cika duniya.
2
Dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa, da dukan kifayen teku, za su riƙa jin tsoronku, suna fargaba. An sa su a cikin hannuwanku.
3
Kome da yake da rai wanda yake tafiya, zai zama abincinku. Kamar yadda na ba ku kowane irin ganye, haka na ba ku kome da kome.
4
“Akwai abu ɗaya da ba za ku ci ba, wato, nama wanda jininsa yake cikinsa tukuna.
5
Game da jinin ranka kuwa lalle zan bukaci lissafi. Zan bukaci lissafi daga kowane dabba. kuma daga kowane mutum, shi ma zan bukaci lissafi game da ran ɗan’uwansa.
6
“Duk wanda ya zub da jinin mutum, ta hannun mutum za a zub da jininsa; gama a cikin siffar Allah ne, Allah ya yi mutum.
7
Amma ku, ku yi ta haihuwa, ku ƙaru; ku yaɗu a duniya, ku yi yawa a bisanta.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options