Skip to content
Farawa 48:13-20

Farawa 48:13-20

13
Yusuf ya ɗauke su biyu, Efraim a damansa zuwa hagun Isra’ila, Manasse kuma a hagunsa zuwa hannun daman Isra’ila, ya kuma kawo su kusa da shi.
14
Amma Isra’ila ya miƙa hannun damansa ya sa shi a kan Efraim, ko da yake shi ne ƙaramin, ta wurin harɗewa hannuwansa, ya sa hannun hagunsa a kan Manasse, ko da yake Manasse ne ɗan farinsa.
15
Sa’an nan ya albarkaci Yusuf ya ce, “Bari Allah a gaban wanda kakannina Ibrahim da Ishaku suka yi tafiya, Allahn da ya zama makiyayina dukan raina zuwa wannan rana,
16
Mala’ikan da ya cece ni daga dukan cuta bari yă albarkaci samarin nan. Bari a kira su da sunana da sunayen kakannina Ibrahim da Ishaku bari kuma su ƙaru ƙwarai a bisa duniya.”
17
Sa’ad da Yusuf ya ga mahaifinsa yana sa hannun damansa a kan Efraim bai ji daɗi ba; saboda haka ya ɗauke hannun mahaifinsa ya cire shi daga kan Efraim zuwa kan Manasse.
18
Yusuf ya ce masa, “A’a, mahaifina, wannan shi ne ɗan farin; ka sa hannunka na dama a kansa.”
19
Amma mahaifinsa ya ƙi ya ce, “Na sani, ɗana, na sani. Shi ma zai zama mutane, zai kuma zama mai girma. Duk da haka ɗan’uwansa zai zama mai girma fiye da shi, kuma zuriyarsa za tă zama ƙungiyar al’ummai.”
20
Ya albarkace su a wannan rana ya ce, “A cikin sunanku Isra’ila zai sa wannan albarka ‘Bari Allah yă sa ku zama kamar Efraim da Manasse.’ ” Saboda haka ya sa Efraim gaban Manasse.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options