Ezekiyel 37:1-11
1
Hannun Ubangiji yana a kaina, ya kuma fitar da ni ta wurin Ruhun Ubangiji ya sa ni a tsakiyar kwarin; yana cike da ƙasusuwa.
2
Ya sa na kai na komo a ciki, na kuma ga ƙasusuwa masu girma da yawa a ƙasar kwarin, ƙasusuwan da suka bushe ƙwarai.
3
Sai ya tambaye ni cewa, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa za su iya rayu?” Ni kuwa na ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai kaɗai ka sani.”
4
Sai ya ce mini, “Ka yi wa waɗannan ƙasusuwa annabci ka ce musu, ‘Busassun ƙasusuwa, ku ji maganar Ubangiji!
5
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce wa waɗannan ƙasusuwa. Zan sa numfashi ya shiga muku, za ku kuwa rayu.
6
Zan harhaɗa muku jijiyoyi in sa muku tsoka in kuma rufe ku da fata; zan sa numfashi a cikinku, za ku kuwa rayu. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
7
Saboda haka sai na yi annabci yadda aka umarce ni. Da nake annabcin, sai aka ji motsi, ƙarar girgiza, sai ƙasusuwan suka harhaɗu, ƙashi ya haɗu da ƙashi.
8
Na duba, sai ga jijiyoyi da nama suka bayyana a kansu fata kuma ta rufe su, amma ba numfashi a cikinsu.
9
Sa’an nan ya ce mini, “Ka yi annabci wa numfashi; ka yi annabci, ɗan mutum, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ka fito daga kusurwoyi huɗu, ya numfashi, ka kuma numfasa cikin waɗannan matattu, don su rayu.’ ”
10
Saboda haka na yi annabci yadda aka umarce ni, sai numfashi ya shiga musu; suka rayu suka kuma miƙe tsaye a ƙafafunsu babbar runduna ce ƙwarai.
11
Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa su ne dukan gidan Isra’ila. Suna cewa, ‘Ƙasusuwanmu sun bushe, sa zuciyarmu duk ya tafi; an share mu ƙaf.’
Settings