Ezekiyel 29:9-10
9
Masar za tă zama kufai. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji. “ ‘Domin ka ce, “Nilu nawa ne; ni na yi shi,”
10
saboda haka ina gāba da kai da rafuffukanka, zan kuma maishe ƙasar Masar ta lalace ta kuma zama kango daga Migdol zuwa Aswan, har iyakar Kush.