Ezekiyel 22:13-16
13
“ ‘Tabbatacce zan tafa hannuwana a kan ƙazamar riba da kika ci da jinin da kin zubar a cikinki.
14
Ƙarfin halinki zai jure ko kuwa hannuwanki za su yi ƙarfi a ranar da na gamu da ke? Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata.
15
Zan watsar da ke cikin al’ummai in warwatsa ke cikin ƙasashe; zan kuma kawo ƙarshen rashin tsarkinki.
16
Sa’ad da ki ƙazantu a idanun al’umma, za ki san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Settings