Kalo te përmbajtja
Ezekiyel 18:20-24

Ezekiyel 18:20-24

20
Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai sami rabo a laifin mahaifi ba, mahaifi ba zai sami rabo a laifi ɗa ba. Adalcin adali zai zama nasa, muguntar mugu za tă koma kansa.
21
“Amma in mugun mutum ya juya daga dukan zunubin da ya aikata ya kuma kiyaye dukan ƙa’idodina ya kuwa yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba.
22
Babu laifin da ya yi da za a tuna da su. Saboda abubuwan adalcin da ya aikata, zai rayu.
23
Ina jin daɗin mutuwar mugu ne? In ji Ubangiji Mai Iko Duka. A maimako, ban fi jin daɗi sa’ad da suka juyo daga hanyoyinsu suka rayu ba?
24
“Amma in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya yi zunubi ya kuma aikata abubuwa masu banƙyamar da mugun mutum ke aikatawa, zai rayu? Babu abubuwan adalcin da ya aikata da za a tuna da su. Saboda rashin amincinsa da kuma saboda zunubai da ya yi, zai mutu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options