Skip to content
Fitowa 8:1-4

Fitowa 8:1-4

1
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka je wurin Fir’auna, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada.
2
In ka ƙi barinsu, zan hore ka da annoban kwaɗi a dukan ƙasarka.
3
Nilu zai cika da kwaɗi. Za su haura zuwa cikin fadanka da kan gadonka, cikin gidajen bayinka da kan mutanenka, cikin kwanonin toye-toyenka da na cin abincinka.
4
Kwaɗin nan za su yi ta tsalle a kanka, da kan mutanenka, da kuma kan dukan bayinka.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options