Fitowa 7:14-19
14
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Zuciyar Fir’auna taurariya ce, ya ƙi yă bar mutanen su tafi.
15
Ka je wurin Fir’auna da safe, yayinda za shi kogi. Ka jira a bakin Nilu don ka sadu da shi, ka ɗauki sandan nan da ya canja zuwa maciji a hannunka.
16
Sa’an nan ka ce masa, ‘Ubangiji, Allah na Ibraniyawa, ya aiko ni in faɗa maka, Ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada a hamada. Amma har yanzu ba ka yi biyayya ba.
17
Ga abin da Ubangiji ya ce, da wannan za ka san cewa ni ne Ubangiji. Da sandan da yake hannuna zan bugi ruwan Nilu, zai kuma zama jini.
18
Kifi a ciki Nilu za su mutu, ruwan kuma zai yi ɗoyi; Masarawa ba za su iya shan ruwansa ba.’ ”
19
Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Ka ɗauki sandanka, ka miƙa hannunka kan ruwan Masar, kan kogunansu da rafuffukansu da kududdufansu da kuma dukan tafkunansu, za su zama jini.’ Jini zai kasance ko’ina a Masar, har ma a cikin abubuwan ajiyar ruwansu da aka yi da itace da kuma dutse.”
Settings