Skip to content
Mai Hadishi 8:1-8

Mai Hadishi 8:1-8

1
Wa yake kama da mai hikima? Wa ya san bayanin abubuwa? Hikima takan haskaka fuskar mutum, ta kuma kawo sakin fuska.
2
Ka yi biyayya da umarnin sarki, na ce, saboda alkawarin da ka yi a gaban Allah.
3
Kada ka yi hanzarin tashi daga gaban sarki. Kada ka kāre abin da ba daidai ba, gama zai iya yin duk abin da ya ga dama.
4
Da yake maganar sarki ita ce mafificiya, wa zai iya ce masa, “Me kake yi?”
5
Duk wanda ya yi biyayya da umarninsa ba zai sami lahani ba, zuciya mai hikima kuma zai san lokacin da ya dace da kuma hanyoyin da suka fi.
6
Gama akwai lokaci da hanyoyin da suka dace da yin kowane abu, ko da yake wahalar mutum ta yi masa yawa.
7
Da yake ba wanda ya san nan gaba, wa zai iya faɗa masa abin da zai faru?
8
Ba wanda yake da iko a kan iska har da zai riƙe ta, saboda haka babu mai iko kan ranar mutuwarsa. Kamar yadda ba a sallamar mutum a lokacin yaƙi, haka ma mugunta ba za tă saki masu aikata ta ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options