Maimaitawar Shari’a 9:8-21
8
A Horeb, kun tayar wa Ubangiji har ya yi fushin da ya isa yă hallaka ku.
9
Sa’ad da na hau kan dutse don in karɓi allunan dutse, allunan alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, na zauna a kan dutse yini arba’in da dare arba’in; ban ci abinci ba, ban sha ruwa ba.
10
Ubangiji ya ba ni alluna biyu wanda shi kansa ya yi rubutu da yatsarsa. A kansu akwai dukan umarnan Ubangiji da an furta muku a kan dutse a tsakiyar wuta, a ranar taron jama’a.
11
A ƙarshen yini arba’in da dare arba’in ɗin, Ubangiji ya ba ni alluna biyu na dutse, allunan alkawari.
12
Sa’an nan Ubangiji ya faɗa mini, “Sauka daga nan da sauri, domin mutanenka waɗanda ka fitar da su daga Masar sun lalace. Sun juye da sauri daga abin da na umarce su, suka kuma yi zubin gunki wa kansu.”
13
Sai Ubangiji ya ce mini, “Na ga mutanen nan, su masu taurinkai ne sosai!
14
Bar ni kawai, in hallaka su, in kuma shafe sunansu daga ƙarƙashin sama. Zan kuwa yi maka wata al’umma mafi ƙarfi da kuma masu yawa fiye da su.”
15
Saboda haka na juya, na sauko daga dutsen yayinda yake cin wuta. Allunan biyu na alkawarin kuma suna a hannuwana.
16
Sa’ad da na duba, sai na ga cewa kun yi zunubi wa Ubangiji Allahnku; kun yi wa kanku gunkin da kuka yi zubi a siffar ɗan maraƙi. Kun kauce da sauri daga hanyar da Ubangiji ya umarce ku.
17
Saboda haka na ɗauko alluna biyun na jefar da su daga hannuwana, na farfashe su a idanunku.
18
Sai nan da nan kuma na fāɗi rubda ciki a gaban Ubangiji, yini arba’in da dare arba’in; ban ci ba, ban sha ba, kamar yadda dā na yi, duka saboda zunubin da kuka aikata a gaban Ubangiji. Ta haka kuka tsokane shi don yă yi fushi.
19
Na ji tsoron fushi da hasalar Ubangiji, gama ya yi fushin da ku da ya isa yă hallaka ku. Amma na yi roƙo a lokacin, Ubangiji kuwa ya saurare ni.
20
Ubangiji ya yi fushi sosai da Haruna, har ya yi niyya yă hallaka shi, amma a wannan lokaci, na yi addu’a saboda Haruna shi ma.
21
Sa’an nan na ɗauki kayan zunubin da kuka yi, wato, gunkin ɗan bijimi, na ƙone shi da wuta, na farfashe shi, na niƙa shi liɓis, sai da ya zama kamar ƙura mai laushi, na zubar da ƙurar a cikin ruwan rafin da yake gangarowa daga dutse.
Settings