Maimaitawar Shari’a 9:25-29
25
Na kwanta rubda ciki a gaban Ubangiji waɗannan yini arba’in da dare arba’in domin Ubangiji ya ce zai hallaka ku.
26
Na yi addu’a ga Ubangiji na ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kada ka hallaka mutanenka, gādon kanka, da ka fansa ta wurin ikonka mai girma, ka kuma fitar da su daga Masar da hannu mai ƙarfi.
27
Ka tuna da bayinka Ibrahim, Ishaku da Yaƙub. Kada ka kula da taurinkan, mugunta da kuma zunubin wannan mutane.
28
In ba haka ba, ƙasar da ka fitar da mu, za tă ce, ‘Domin Ubangiji bai iya kai su cikin ƙasar da ya yi musu alkawari ba ne, kuma domin ya ƙi su, shi ya sa ya fitar da su ya kashe su a hamada.’
29
Amma su mutanenka ne, gādonka da ka fitar ta wurin ikonka mai girma, da kuma hannunka mai ƙarfi.”
Settings