Maimaitawar Shari’a 4:23-26
23
Ku yi hankali kada ku manta da alkawarin da Ubangiji Allahnku ya yi da ku; kada fa ku yi wa kanku gunki a kamannin wani abin da Ubangiji Allahnku ya hana.
24
Gama Ubangiji Allahnku wuta ne mai ƙuna, Allah ne mai kishi.
25
Bayan kun haifi ’ya’ya da jikoki, kuka kuma zauna na dogon lokaci a ƙasar, in har kuka lalace, kuka kuma yi wani irin gunki, kuna aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnku, kuna kuma sa shi fushi.
26
Yau, na kira sama da duniya, su zama shaidata a kanku. Idan kuka yi rashin biyayya, lalle za ku hallaka nan da nan daga ƙasar da kuke ƙetare Urdun ku gāda. Ba za ku daɗe a cikinta ba, amma za a kawar da ku ƙaƙaf.
Settings