Maimaitawar Shari’a 29:10-11
10
Yau, ga ku nan tsaye, dukanku a gaban Ubangiji Allahnku, shugabanninku da manyan mutanenku, dattawanku da hafsoshinku, da kuma dukan sauran mutanen Isra’ila,
11
tare da ’ya’yanku da matanku, da baƙin da suke zama sansanoninku, har ma da waɗanda suke muku faskare, da waɗanda suke ɗiba muku ruwa.