Skip to content
Maimaitawar Shari’a 1:34-40

Maimaitawar Shari’a 1:34-40

34
Da Ubangiji ya ji abin da kuka faɗa, sai ya husata, ya kuma yi rantsuwa ya ce,
35
“Babu wani a cikin wannan muguwar tsara da zai ga ƙasa mai kyau da na rantse zan ba wa kakanninku,
36
sai dai Kaleb ɗan Yefunne. Zai gan ta, zan ba shi duk ƙasar da tafin ƙafarsa ta taka, shi da zuriyarsa, gama ya bi Ubangiji da zuciya ɗaya.”
37
Saboda ku Ubangiji ya husata da ni, ya kuma ce, “Kai ma, ba za ka shiga ƙasar ba.
38
Amma mataimakinka, Yoshuwa ɗan Nun, zai shiga. Ka ƙarfafa shi gama shi ne zai jagoranci Isra’ila su gāje ta.
39
Amma ’ya’yanku ƙanana waɗanda ba su san mugunta ko nagarta ba, waɗanda kuke tsammani za a kwashe su ganima, su za su shiga ƙasar. Zan ba da ita gare su, za su kuwa mallake ta.
40
Amma ku kam, sai ku juya, ku koma cikin hamada ta hanyar Jan Teku.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options