Ayyukan Manzanni 13:14-16
14
Daga Ferga kuwa suka ci gaba zuwa Antiyok na Fisidiya. A ranar Asabbaci sai suka shiga majami’a suka zauna.
15
Bayan an yi karatu daga cikin Doka, da kuma Annabawa, sai shugabannin majami’ar suka aika musu suka ce, “’Yan’uwa, in kuna da wani saƙon ƙarfafawa domin jama’a, sai ku yi.”
16
Yana miƙewa tsaye, sai Bulus ya yi musu alama da hannu ya ce, “Mutanen Isra’ila da kuma ku Al’ummai da kuke wa Allah sujada, ku saurare ni!
Settings