2 Sama’ila 18:9-15
9
To, Absalom ya haɗu da mutanen Dawuda. Yana hawan dokinsa, kuma yayinda dokin ya kusa kai cikin rassan babban itacen oak, sai kan Absalom ya sarƙafe a kan itacen oak ɗin. Dokin ya wuce da gudu, shi kuwa ya rataye a can yana lilo.
10
Sa’ad da wani daga cikin mutanen ya gan haka, sai ya gaya wa Yowab, “Na ga Absalom yana rataye a itacen oak.”
11
Yowab ya ce wa mutumin da ya ba shi labarin, “Mene! Ka ga shi? Don me ba ka buge shi har ƙasa nan da nan ba? Ai, da na ba ka shekel goma na azurfa da abin ɗamarar jarumi.”
12
Amma mutumin ya ce wa Yowab, “Ko da za a auna mini azurfa dubu a hannuna, ba zan miƙa hannuna in taɓa ɗan sarki ba. A kunnuwanmu fa sarki ya umarce ka, da Abishai, da Ittai cewa, ‘Ku tsare saurayin nan Absalom a madadina.’
13
Da na yi haka da na sa kaina a halin ƙaƙa-ni-ka-yi, kuma babu abin da zai ɓoyu ga sarki, kai kuwa za ka janye abinka daga gare ni.”
14
Yowab ya ce, “Ba zan ɓata lokaci da kai ba.” Saboda haka sai ya ɗauki māsu uku a hannunsa ya zura su a ƙahon zuciyar Absalom, tun Absalom yana da sauran rai a maƙale a itacen oak.
15
Masu ɗaukan kayan yaƙin Yowab goma kuwa sun kewaye Absalom, suka bubbuge shi suka kashe.
Settings