2 Sarakuna 17:29-33
29
Duk da haka, jama’ar kowace ƙasa, suka ƙera tasu alloli a garuruwa masu yawa inda suke zaune, suka sa su a masujadan da mutanen Samariya suka gina a kan tuddai.
30
Mutane daga Babilon suka ƙera Sukkot Benot, mutane daga Kut suka ƙera Nergal, mutane daga Hamat suka ƙera Ashima;
31
Awwiyawa suka ƙera Nibhaz da Tartak, Sefarfayawa kuwa suka ƙone ’ya’yansu a wuta a matsayi hadayu ga Adrammelek da Anammelek allolin Sefarfayim.
32
Sun yi wa Ubangiji sujada, amma kuma suka zaɓi mutanensu su yi musu hidima a matsayin firistoci a masujadan da suke kan tuddai.
33
Sun yi wa Ubangiji sujada, amma kuma sun bauta wa allolinsu bisa ga al’adun ƙasashen da suka fito.
Settings