2 Sarakuna 1:2-8
2
Ahaziya fa ya fāɗo daga tagar ɗakin samansa a Samariya ya ji rauni. Saboda haka ya aiki masinjoji, yana cewa, “Ku je ku tuntuɓi Ba’al-Zebub, allahn Ekron, ku ga ko zan warke daga wannan rauni.”
3
Amma mala’ikan Ubangiji ya ce wa Iliya mutumin Tishbe, “Ka haura ka taryi masinjojin sarkin Samariya, ka tambaye su, ‘Don babu Allah ne a Isra’ila da za ku tafi ku tuntuɓi Ba’al-Zebub allahn Ekron?’
4
Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ba za ka tashi daga inda kake kwance ba, ba shakka za ka mutu!’ ” Iliya ya yi kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, sai ya tafi.
5
Da masinjojin suka koma wurin sarki, sai sarki ya ce da su, “Don me kuka komo?”
6
Sai suka amsa, “Wani mutum ya sadu da mu ya ce mana, ‘Ku koma wurin sarkin da ya aike ku, ku ce masa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, don babu Allah ne a Isra’ila da ka aika a tuntuɓi Ba’al-Zebub allahn Ekron? Saboda haka ba za ka tashi daga gadon da kake kwance ba. Ba shakka za ka mutu!” ’ ”
7
Sai Sarkin ya tambaye su ya ce, “Wanda irin mutum ne ya yi muku wannan magana?”
8
Sai suka ce, “Mutumin ya sa riga mai gashi, ya kuma yi ɗamara da fata.” Sarkin ya ce, “Ai, Iliya mutumin Tishbe nan ne.”
Settings