2 Tarihi 7:12-16
12
sai Ubangiji ya bayyana gare shi a daren ya ce, “Na ji addu’arka na kuma zaɓi wannan wuri don kaina, a matsayin haikali don hadayu.
13
“Sa’ad da na kulle sammai don kada a yi ruwan sama ko na umarci fāri su cinye amfanin ƙasar ko kuwa na aika da annoba a cikin mutanena,
14
in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu.
15
Yanzu, idanuna za su buɗu, kunnuwata kuma za su saurara ga addu’o’in da aka miƙa a wannan wuri.
16
Na zaɓi na kuma tsarkake wannan haikali saboda Sunana yă kasance a can har abada. Idanuna da kuma zuciyata kullum za su kasance a can.
Settings