1 Sarakuna 13:1-5
1
Bisa ga umarnin Ubangiji, sai wani mutumin Allah ya zo daga Yahuda zuwa Betel, yayinda Yerobowam yake tsaye kusa da bagade don yă miƙa hadaya.
2
Sai mutumin Allah ya tā da murya a kan bagade bisa ga umarnin Ubangiji ya ce, “Ya bagade, bagade! Ubangiji ya ce, ‘Za a haifi ɗa mai suna Yosiya wa gidan Dawuda. A kanka zai miƙa firistoci na masujadai kan tuddai masu miƙa hadayu a nan, za a kuma ƙone ƙasusuwan mutane a kanka.’ ”
3
A wannan rana mutumin Allah ya ba da alama, “Ga alamar da Ubangiji ya furta. Wannan bagade zai tsage yă rabu kashi biyu, tokar da yake a kansa za tă zuba a ƙasa.”
4
Sa’ad da Yerobowam ya ji abin da mutumin Allah ya tā da murya ya faɗa game da bagaden Betel, sai ya miƙa hannunsa daga bagaden ya ce, “Ku kama shi!” Amma sai hannun da ya miƙa ya yanƙwane, har bai iya janye shi ba.
5
Haka ma, bagaden ya rabu, tokarsa kuma ya zuba, bisa ga alamar da mutumin Allah ya bayar, ta wurin kalmar Ubangiji.
Settings