1 Yohanna 5:6-9
6
Ga wanda ya zo ta wurin ruwa da jini, wato, Yesu Kiristi. Bai zo ta wurin ruwa kaɗai ba, sai dai ta wurin ruwa da kuma jini. Ruhu ne kuwa yake ba da shaida, gama Ruhu shi ne gaskiya.
7
Akwai shaidu uku, wato,
8
Ruhu, da ruwa, da kuma jini; waɗannan uku kuwa manufarsu ɗaya ce.
9
Tun da yake mukan yarda da shaida mutane, ai, shaidar Allah ta fi ƙarfi. Wannan ita ce shaidar Allah, wato, ya shaidi Ɗansa.
Settings