1 Korintiyawa 1:26-31
26
’Yan’uwa, ku tuna yadda kuke sa’ad da aka kira ku. Babu masu hikima da yawa a cikinku, bisa ga ganin mutum; babu masu iko da yawa, babu masu martaba da yawa bisa ga haihuwa.
27
Amma Allah ya zaɓi abubuwa masu wautata duniya, don yă kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abubuwa marasa ƙarfi na duniya, domin ya ba wa masu ƙarfi kunya.
28
Ya zaɓi abubuwa marasa martaba na wannan duniya da kuma abubuwan da aka rena da abubuwan da ba a ɗauka a bakin kome ba, domin a wofinta abubuwan da ake ganinsu da daraja,
29
domin kada wani ya yi taƙama a gabansa.
30
Saboda Allah ne kuke cikin Kiristi Yesu, shi wanda ya zama hikima a gare mu daga Allah. Kiristi shi ne adalcinmu, da tsarkinmu, da kuma fansarmu.
31
Saboda haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Duk wanda yake taƙama, ya yi taƙama a cikin Ubangiji.”
Settings