Zabura14
Listen to this chapter
0:00
0:00
1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Wawaye sukan ce a ransu, “Ba Allah.” Sun lalace, ayyukansu kuwa mugaye ne; babu wani da yake yi abu mai kyau.
2
Ubangiji ya duba daga sama a kan ’yan adam don yă ga ko akwai wani da ya gane, wani wanda yake neman Allah.
3
Duka sun kauce, duka gaba ɗaya sun zama lalatattu; babu ɗaya wanda yake yin abu mai kyau, ba ko ɗaya.
4
Masu aikata mugunta za su taɓa koyo. Suna cin mutane yadda mutane ke cin gurasa kuma waɗanda ba sa kira bisa Ubangiji?
5
Ga su, tsoro ya sha kansu, gama Allah yana cikin ƙungiyar adalai.
6
Ku masu mugunta kuna sa ƙoƙarin matalauta yă zama banza, amma Ubangiji ne mafakansu.
7
Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana! Sa’ad da Ubangiji zai maido da sa’ar mutanensa, bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna!
Use ← → arrow keys to navigate
Settings
Reading Style
Typeface
Font Size px
Options
Study Note